22 Agusta 2020 - 11:04
Ana Ci Gaba Da Yin Tsokaci Akan Tsagaita Wutar Yaki A Kasar Libya

A jiya Juma’a ne dai shugaban majalisar wakilan kasar Libya Aqila Saleh ya kira yi dukkanin bangarorin da suke yaki da su tsagaita wuta.

ABNA24 : Shi kuwa Fathi Bashaqaha wanda shi ne ministan harkokin cikin gidan kasar Libya, ya bayyana cewa; Ba domin taimakon Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiya da kuma Masar ba, to da ba a kai ga cimma tsagaita wutar yaki ba a Libya.

A wata hira da tashar talabijin din Bloomberg ta yi da shi, Bashaqaha ya kara da cewa; Abinda ya kamata ya biyo bayan tsagaita wutar shi ne tattauna wacce za ta kai ga samun kwanciyar hankali, kuma wajibi ne a dauki wadannan matakan da gaggawa.

Tun da fari, a jiya Juma’a ne shugaban kasar ta Libya Fayez Al-Sarraj, da kuma kakakin Majalisar wakilai Aquila Saleh su ka yi kira da a tsagaita wutar yaki, bayan tuntubar juna da aka yi akan rikicin kasar ta Libya.

Bugu da kari Al-Sarraj da Saleh sun yi kira da a dawo da hako man fetur da tace shi domin fitar da shi zuwa kasuwannin duniya.

342/